Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 28:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ishaku ya kira Yakubu ya sa masa albarka, ya umarce shi da cewa, “Ba za ka auri ɗaya daga cikin 'ya'yan matan Kan'aniyawa ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Saboda haka Ishaku ya kira Yaƙub, ya kuma albarkace shi, sa’an nan ya umarce shi ya ce, “Kada ka auri mace daga Kan’ana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 28:1
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

ka rantse da Ubangiji na sama da duniya, cewa ba za ka auro wa ɗana mata daga 'yan matan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a tsakaninsu ba.


Rifkatu kuwa ta ce wa Ishaku, “Na gaji da raina saboda matan Hittiyawa. Idan Yakubu zai auri ɗaya daga cikin waɗannan mata na Hittiyawa, wato daga matan ƙasar, wane amfani raina zai daɗa mini?”


Maigidana ya rantsar da ni da cewa, ‘Ba za ka auro wa ɗana mace daga cikin 'ya'yan Kan'aniyawa waɗanda nake zaune a ƙasarsu ba,


sai 'ya'yan Allah suka ga 'yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.


Musa ya riga ya ba rabin kabilar Manassa gādo a Bashan, sauran rabin kabilar kuwa Joshuwa ya ba su gādo tare da 'yan'uwansu a yammacin hayin Urdun. Sa'ad da Joshuwa ya sallame su zuwa gida, ya sa musu albarka,


Wannan ita ce albarkar da Musa, mutumin Allah, ya sa wa Isra'ilawa kafin ya rasu.


Waɗannan duka su ne kabilan Isra'ila goma sha biyu, wannan kuma shi ne abin da mahaifinsu ya faɗa musu sa'ad da yake sa musu albarka. Ya sa wa kowannensu albarka da irin albarkar da ta cancance shi.


Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce, “Allah na Ibrahim da Ishaku, Iyayena da suka yi tafiyarsu a gabansa, Allah da ya bi da ni Dukan raina har wa yau, ya sa musu albarka.


Sa'an nan za mu ba ku auren 'ya'yanmu mata, mu kuma mu auro wa kanmu 'ya'yanku mata. Sai kuwa mu zauna tare da ku, mu zama jama'a ɗaya.


Ku yi aurayya da mu. Ku ba mu 'yan matanku, ku kuma ku auri 'yan matanmu.


ka shirya mini abinci mai daɗi irin wanda nake so, ka kawo mini in ci, don in sa maka albarka kafin in rasu.”


Amma za ka tafi ƙasata, daga cikin dangina ka auro wa ɗana Ishaku mata.”


Yanzu Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka, ya kuwa sallame shi zuwa Fadan-aram domin ya auro mace daga can. Da Isuwa ya ga Ishaku ya sa wa Yakubu albarka ya kuma umarce shi da cewa, “Ba za ka auro wata daga cikin 'yan matan Kan'aniyawa ba,”


A can, sai Yahuza ya ga 'yar wani Bakan'ane mai suna Shuwa. Ya aure ta, ya shiga wurinta,


Ku auri mata, ku haifi 'ya'ya mata da maza. Ku auro wa 'ya'yanku mata, ku aurar da 'ya'yanku mata, domin su haifi 'ya'ya mata da maza, ku riɓaɓɓanya a can, kada ku ragu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ