8 Yanzu fa, ɗana, ka biye wa maganata yadda zan umarce ka.
8 Saboda haka ɗana, ka saurara da kyau ka kuma yi abin da na faɗa maka.
Ku 'ya'ya, ku yi wa iyayenku biyayya tsakani da Ubangiji, domin wannan shi ne daidai.
Sai mahaifiyarsa ta ce masa, “La'anarka ta faɗo bisa kaina, ɗana. Kai dai ka yi biyayya da maganata. Je ka, ka kamo mini.”
Amma Bitrus da manzannin suka amsa suka ce, “Wajibi ne mu yi wa Allah biyayya fiye da mutum.
Amma Bitrus da Yahaya suka mayar musu da jawabi suka ce, “To, in daidai ne a gun Allah mu fi jin taku da ta Allah, sai ku duba ku gani.
Domin haka, ɗana, ka ji muryata, ka tashi ka gudu zuwa wurin Laban ɗan'uwana a Haran,
Sai Ubangiji ya ce mata, “Al'umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.”
‘Kawo mini nama, ka shirya mini abinci mai daɗi in ci, in sa maka albarka a gaban Ubangiji kafin in rasu.’
Je ka garke, ka kamo 'yan awaki biyu kyawawa, domin in shirya abinci mai daɗi da su domin mahaifinka, irin wanda yake so.