A waɗannan shekaru ashirin da nake cikin gidanka, na yi maka barantaka shekara goma sha huɗu domin 'ya'yanka mata biyu, shekara shida kuma domin garkenka, ka kuwa sauya ladana har sau goma.
Ubangiji Allah Mai Runduna Ya taɓi duniya, ta girgiza. Duk waɗanda suke zaune cikinta Suna baƙin ciki. Duniya duka takan hau Ta kuma gangara kamar ruwan Kogin Nilu.