Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 27:40 - Littafi Mai Tsarki

40 Ta wurin takobinka za ka rayu Za ka yi wa ɗan'uwanka barantaka, Amma sa'ad da ka ɓalle, Za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 Za ka rayu ta wurin takobi za ka kuwa bauta wa ɗan’uwanka. Amma sa’ad da ka ɓalle, za ka kakkarye karkiyarsa daga wuyanka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 27:40
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Ubangiji ya ce mata, “Al'umma biyu suke a cikin mahaifarki, mutum biyu da za ki haifa, za su rabu da juna, ɗayan zai fi ɗayan ƙarfi, babban zai bauta wa ƙaramin.”


Har wa yau Edom ya tayar wa Yahuza. A wannan lokaci kuma Libna ta tayar wa mulkinsa, saboda Yoram ya rabu da bin Ubangiji Allah na kakanninsa.


Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a ƙasar Edom duka. Edomawa suka zama talakawan Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara duk inda ya tafi.


Amma zan yi amfani da Mowab kamar kwanon wanki, Edom kuwa kamar akwatin takalmina. Zan yi sowar nasara a kan Filistiyawa.”


A zamaninsa Edomawa suka tayar wa Yahuza, suka naɗa wa kansu sarki.


Gama Edomawa suka sāke kai wa Yahuza yaƙi, suka kama mutane suka tafi da su.


Yanzu kai, Amaziya, ka bugi Edomawa don haka zuciyarka ta kumbura. To ka gode da darajar da ka samu, ka tsaya a gida, gama don me kake tonon rikici da zai jawo maka fāduwa, kai da mutanen Yahuza?”


Ya kuma kashe Edomawa dubu goma (10,000) a Kwarin Gishiri, sa'an nan ya ƙwace Sela, ya ba ta suna Yokteyel, haka ake kiranta har wa yau.


Jakadun kuwa suka komo wurin Yakubu, suka ce, “Mun je wurin ɗan'uwanka Isuwa, yana kuwa zuwa ya tarye ka da mutum arbaminya tare da shi.”


“Kada dai ku zaci na zo ne in kawo salama a duniya. A'a, ban zo domin in kawo salama ba, sai dai takobi.


Bari jama'a su bauta maka, Al'ummai kuma su sunkuya maka. Za ka yi shugabancin 'yan'uwanka, Allah ya sa 'ya'yan mahaifiyarka su sunkuya maka. La'ananne ne dukan wanda ya la'anta ka, Albarkatacce ne dukan wanda ya sa maka albarka.”


Amma Isuwa ya ce, “Ina da abin da ya ishe ni, ɗan'uwana, riƙe abin da kake da shi don kanka.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ