A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.
Ashe, ba dukanmu Ubanmu ɗaya ba ne? Ba Allah nan ɗaya ya halicce mu ba? To, me ya sa muke keta alkawarin da muka yi wa junanmu, muna raina alkawarin da Allah ya yi wa kakanninmu?
Saboda haka, yanzu sai ku kirawo mini dukan annabawan Ba'al, da dukan masu yi masa sujada, da dukan firistocinsa. Kada a manta da wani, gama ina da babbar hadayar da zan miƙa wa Ba'al. Duk wanda bai zo ba, za a kashe shi.” Amma dabara ce Yehu yake yi don ya hallaka waɗanda suke yi wa Ba'al sujada.
Ishaku kuwa ya yi makyarkyata ƙwarai, ya ce, “Wane ne wannan fa, da ya farauto naman ya kawo mini, na kuwa cinye kafin ka zo, har na sa masa albarka? – I, albarkatacce zai zama.”
“Bari kowane mutum ya yi hankali da maƙwabcinsa, Kada kuma ya amince da kowane irin ɗan'uwa, Gama kowane ɗan'uwa munafuki ne, Kowane maƙwabci kuma mai kushe ne.
Da gari ya waye kuma ga shi, ashe, Lai'atu ce. Sai Yakubu ya ce wa Laban, “Mene ne wannan da ka yi mini? Ba don Rahila na yi maka barantaka ba? Don me ka yaudare ni?”