Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 27:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Don haka ya zo kusa ya sumbace shi. Ishaku ya sansana rigunansa, ya sa masa albarka, ya ce, “Duba, ƙanshin ɗana Yana kama da ƙanshin jeji Wanda Ubangiji ya sa wa albarka!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Saboda haka ya je gunsa ya sumbace shi. Sa’ad da Ishaku ya ji ƙanshin rigunansa, sai ya sa masa albarka ya ce, “Aha, ƙanshin ɗana yana kama da ƙanshin jejin da Ubangiji ya sa wa albarka ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 27:27
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ƙasa ma da take shanye ruwan da ake yi mata a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda ake noma ta dominsu, Allah yakan sa mata albarka.


Ka kwarara ruwa mai yawa a gonakin da aka nome, Ka jiƙe su da ruwa, Ka tausasa ƙasar da yayyafi, Ka sa ƙananan tsire-tsire su yi girma.


Ishaku ya yi shuka a waccan ƙasar, a shekaran nan kuwa ya girbe cikakken amfani. Ubangiji ya sa masa albarka,


Ta wurin bangaskiya Ishaku ya sa wa Yakubu da Isuwa albarka a kan al'amuran da za su zo.


'Ya'yan ɓaure sun nuna, Tohon inabi yana ƙanshi. Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa!


Rifkatu ta ɗauki riguna mafi kyau na babban ɗanta Isuwa waɗanda suke wurinta cikin gida, ta kuwa sa wa Yakubu ƙaramin ɗanta su,


Mahaifinsa Ishaku kuwa ya ce masa, “Zo kusa ka sumbace ni, ɗana.”


Yanzu fa, idanun Isra'ila sun dushe saboda yawan shekaru, har ba ya iya gani. Sai Yusufu ya kawo su kusa da shi, ya sumbace su ya rungume su.


A kan Yusufu, ya ce, “Ubangiji ya sa wa ƙasarsa albarka, Da kyawawan kyautai daga sama, da raɓa, Da ruwan da yake a ƙasa,


Sai Ishaku mahaifinsa ya amsa masa ya ce, “Ga shi, ni'imar ƙasar za ta nisanci mazauninka, Raɓar samaniya can ƙwanƙoli za ta nisance ka.


Sai ya sa wa Yusufu albarka, ya ce, “Allah na Ibrahim da Ishaku, Iyayena da suka yi tafiyarsu a gabansa, Allah da ya bi da ni Dukan raina har wa yau, ya sa musu albarka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ