Don haka ya zo kusa ya sumbace shi. Ishaku ya sansana rigunansa, ya sa masa albarka, ya ce, “Duba, ƙanshin ɗana Yana kama da ƙanshin jeji Wanda Ubangiji ya sa wa albarka!
Sai Yowab ya tafi wurin sarki, ya faɗa masa. Sarki ya sa a kira Absalom. Absalom kuwa ya zo gaban sarki, ya rusuna har ƙasa. Sarki kuwa ya marabce shi, ya yi masa sumba.