Dawuda ya ce masa, “Na zo aikin sarki ne, ya kuwa ce kada in sanar wa kowa abin da ya aiko ni in yi. Jama'ata kuwa na riga na shirya inda zan sadu da su.
Sa, an nan tsohon annabin ya ce masa, “Ai, ni ma annabi ne kamarka. Ubangiji ya yi mini magana ta bakin wani mala'ika, ya ce mini in komar da kai gidana don ka ci abinci, ka sha ruwa.” Amma ƙarya ce ya yi masa.