A lokacin nan sai sarki Hezekiya ya kamu da rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya, ɗan Amoz, ya je wurinsa domin ya gaishe shi, ya ce masa, “Ubangiji ya ce ka kintsa kome daidai, gama ba za ka warke ba. Ka yi shirin mutuwa.”
Amma Dawuda ya rantse masa, ya ce, “Mahaifinka ya hakikance na sami tagomashi a wurinka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada ya baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji da kai kuma, mataki ɗaya yake tsakanina da mutuwa!”
A sa'ad da lokaci ya gabato da Isra'ila zai mutu, ya kira ɗansa Yusufu ya ce masa, “Idan zan sami tagomashi a idonka, ka sa hannunka a ƙarƙashin cinyata, ka ɗau alkawari za ka aikata mini aminci da gaskiya. Kada ka binne ni a Masar,