Suka ce, “Lalle, mun gani a fili Ubangiji yana tare da kai, saboda haka muke cewa bari rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai, bari kuma mu ƙulla alkawari da kai,
Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.
Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-sheba. Kada ku yi ƙoƙarin nemana a Betel, Gama Betel lalacewa za ta yi. Kada ku tafi Gilgal, Gama an ƙaddara wa jama'arta su yi ƙaura.”