30 Sai ya shirya musu liyafa, suka ci suka sha.
30 Sai Ishaku ya shirya musu liyafa, suka ci suka kuma sha.
Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka ratse suka shiga gidansa, ya shirya musu liyafa, ya toya musu abinci marar yisti, suka ci.
Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji.
In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.
Yakubu kuwa ya miƙa hadaya a bisa dutsen, ya kirawo iyalinsa su ci abinci, suka kuwa ci abinci suka zauna dukan dare a bisa dutsen.
Ku riƙa yi wa juna baƙunta, ba tare da ƙunƙuni ba.
Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.
Suka tashi tun da sassafe suka rantse wa juna, Ishaku ya sallame su, suka tafi cikin salama.
Yetro, surukin Musa kuwa, ya miƙa hadaya ta ƙonawa da sadaka ga Allah. Sai Haruna ya zo tare da dattawan Isra'ila duka don su ci abinci tare da surukin Musa a gaban Allah.