Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 26:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Da daren nan Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan sa maka albarka in riɓaɓɓanya zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 A wannan dare Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka Ibrahim. Kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan albarkace ka, zan kuma ƙara yawan zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 26:24
41 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya kuma ce, “Ni ne Allah na kakanninka, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” Sai Musa ya ɓoye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi Allah.


“Zan kafa alkawarina da kai, da zuriyarka a bayanka cikin dukan tsararrakinsu, madawwamin alkawari ke nan, in zama Allahnka da na zuriyarka a bayanka.


Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”


‘Ni ne Allahn kakanninka, Allahn Ibrahim da Ishaku da Yakubu.’ Sai jikin Musa ya ɗauki rawa, bai kuma iya ƙarfin halin dubawa ba.


Sai ya ce, “Ya Ubangiji Allah na maigidana Ibrahim.


Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,


Ga shi kuwa, Ubangiji na tsaye a kansa yana cewa, “Ni ne Ubangiji, Allah na Ibrahim, mahaifinka, da Ishaku, ƙasar da kake kwance a kai, zan ba ka ita da zuriyarka.


Zan mai da zuriyarka kamar turɓayar ƙasa, har in mutum ya iya ƙidaya turɓayar ƙasa, to, a iya ƙidaya zuriyarka.


Saboda haka, ma iya fitowa gabagaɗi, mu ce, “Ubangiji shi ne mataimakina, Ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”


“Ya ku ɗan ƙaramin garke, kada ku ji tsoro, domin Ubanku na jin daɗin ba ku rabo a cikin Mulkin.


‘Ni ne Allahn Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.’ Ai, waɗanda Allah shi ne Allahnsu rayayyu ne, ba matattu ba.”


Ni ne Ubangiji wanda ya halicce ku, Tun farko, na taimake ku. Kada ku ji tsoro, ku bayina ne, Zaɓaɓɓun mutanena waɗanda nake ƙaunarsu.


Kada ka ji tsoro, ina tare da kai, Ni ne Allahnka, kada ka bar kome ya firgita ka. Zan sa ka yi ƙarfi, in kuma taimake ka, Zan kiyaye ka, in cece ka.


Allah ne Mai Cetona, Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba. Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi, Shi ne Mai Cetona.”


ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni.


Ubangiji ya ce, “Ni ne wanda yake ƙarfafa ku. Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa, Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?


“Ku kasa kunne gare ni, ku da kuka san abin da yake daidai, Ku da kuke riƙe da koyarwata a zuciyarku. Kada ku ji tsoro sa'ad da mutane suke yi muku ba'a da zagi.


Sai Ibrahim ya koma wurin samarinsa. Suka tashi suka tafi Biyer-sheba tare. Ibrahim ya yi zamansa a Biyer-sheba.


Amma bisa ga hakika sun ɗokanta ne a kan wata ƙasa mafi kyau, wato ta Sama. Saboda haka ne, Allah ba ya jin kunya a ce da shi Allahnsu, don kuwa ya shirya musu birni.


Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”


Allah kuwa ya ji muryar yaron, mala'ikan Allah kuma ya kira Hajaratu daga sama, ya ce mata, “Me yake damunki, Hajaratu? Kada ki ji tsoro gama Allah ya ji muryar yaron a inda yake.


hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,


Allah Maɗaukaki ya sa maka albarka, ya sa ka hayayyafa ya riɓaɓɓanya ka, ka zama ƙungiyar jama'o'i,


Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”


Amma Laban ya ce masa, “Da za ka yarda mini, sai in ce, na fahimta bisa ga istihara, cewa Ubangiji ya sa mini albarka saboda kai.


Isra'ila ya kama tafiyarsa da dukan abin da yake da shi. Ya zo Biyer-sheba, ya kuwa ba da hadayu ga Allah na mahaifinsa Ishaku.


Kada ku ɗauka daga cikin abin da aka haramta don zafin fushin Ubangiji ya huce, ya yi muku jinƙai, ya ji tausayinku, ya kuma riɓaɓɓanya ku ma kamar yadda ya rantse wa kakanninku,


Ubangiji yana tare da Yusufu, har ya zama mutum ne mai galaba a gidan maigidansa Fotifar, Bamasaren.


Maigidansa kuwa ya ga Ubangiji yana tare da shi, Ubangiji kuma yakan sa albarka ga aikin hannuwansa duka.


Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.


sa'an nan zan tuna da alkawarina wanda na yi wa Yakubu, da Ishaku, da Ibrahim, zan kuwa tuna da ƙasar.


Amma saboda su zan tuna da alkawarin da na yi da kakanninsu waɗanda na fisshe su daga ƙasar Masar a idon al'ummai domin in zama Allahnsu. Ni ne Ubangiji.”


Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali, kada ku ji tsoro, ko ku firgita saboda su, gama Ubangiji Allahnku yana tare da ku. Ba zai kunyatar da ku ba, ba kuwa zai yashe ku ba.”


Yanzu dai, 'yata, kada ki damu, zan yi miki dukan abin da kika roƙa, gama dukan mutanen garin sun sani ke macen kirki ce.


Amma Iliya ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, ki tafi, ki yi yadda kika ce, amma ki fara yi mini 'yar waina, ki kawo mini, sa'an nan ki yi wa kanki da ɗanki.


Sa'ad da na yi kira gare ka, ka zo kusa. Sa'an nan ka ce mini kada in ji tsoro.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ