13 har mutumin ya arzuta, ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.
13 Mutumin ya arzuta, arzikinsa ya yi ta haɓaka har ya zama attajiri.
Albarkar Ubangiji takan arzuta mutum, amma yawan aiki ba shi yake kawo arziki ba.
Iyalinsa za su zama attajirai masu dukiya, Adalcinsa zai tabbata har abada.
Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai.
Ta haka mutumin ya zama riƙaƙƙen mai arziki, yana da manya manyan garkuna da barori mata da maza, da raƙuma, da jakuna.
Yanzu Abram ya arzuta da dabbobi, da azurfa, da zinariya.