Abram kuwa ya kama hanya bisa ga faɗar Ubangiji, Lutu kuma ya tafi tare da shi, Abram yana da shekara saba'in da biyar sa'ad da ya yi ƙaura daga Haran.
Yakubu ya ce wa Fir'auna, “Shekaruna na zaman baƙuncina, shekara ce ɗari da talatin, shekaruna kima ne cike kuma da wahala, ba su kuwa kai yawan shekarun kakannina ba, cikin baƙuncinsu.”
Sai Ishaku ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya rasu, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi, da kyakkyawan tsufa cike da kwanaki, 'ya'yansa Isuwa da Yakubu suka binne shi.