In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.
Ya hau kan tsaunuka Tare da ɗumbun waɗanda ya kamo daga yaƙi, Yana karɓar kyautai daga wurin mutane, Daga wurin 'yan tawaye kuma. Ubangiji Allah zai zauna a can.
Ubangiji ya sa wa maigidana albarka ƙwarai, ya kuwa zama babba, ya ba shi garkunan tumaki da na shanu, da azurfa da zinariya, da barori mata da maza, da raƙuma da jakai.