Ya kuma yi masa alkawari game da kaciya. Ta haka, da Ibrahim ya haifi Ishaku, ya yi masa kaciya a rana ta takwas. Ishaku ya haifi Yakubu, Yakubu kuma ya haifi kakanninmu sha biyun nan.
'Ya'ya maza na Ketura, wato ƙwarƙwarar Ibrahim, su ne Zimran, da Yokshan, da Medan, da Madayana, da Yisbak, da Shuwa. 'Ya'yan Yokshan, maza, su ne Sheba, da Dedan.