ta ce wa baran, “Wane ne mutumin can da yake zuwa daga saura garin ya tarye mu?” Sai baran ya ce, “Ai, maigidana ne.” Ta ɗauki mayafinta ta yi lulluɓi.
Ishaku kuwa ya shiga da ita cikin alfarwarsa ya ɗauki Rifkatu ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta. Ta haka Ishaku ya ta'azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.