Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 24:32 - Littafi Mai Tsarki

32 Mutumin ya shiga gidan, Laban kuwa ya sauke raƙuman, ya ba shi baro da harawa domin raƙuma, da ruwa ya wanke ƙafafunsa da ƙafafun waɗanda suke tare da shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

32 Don haka mutumin ya tafi gidan, aka kuma saukar da kaya kan raƙuman. Aka kawo wa raƙuman ciyawa da abincin dabbobi, aka kuma kawo ruwa dominsa da mutanensa su wanke ƙafafunsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 24:32
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya kai su gidansa, ya ba jakan harawa, aka wanke ƙafafun baƙin, sa'an nan suka ci suka sha.


Da mutumin ya kawo su gidan Yusufu, ya ba su ruwa, suka kuwa wanke ƙafafunsu, sa'an nan kuma ya bai wa jakunansu tauna,


Bari a kawo ɗan ruwa ku wanke ƙafafunku, ku shaƙata a gindin itace,


wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi 'ya'ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari.


Da ya waiwaya wajen matar, ya ce wa Saminu. “Ka ga matan nan? Na shigo gidanka, ba ka ba ni ruwan wanke ƙafa ba, amma ita ta zub da hawayenta a ƙafafuna, ta kuma goge su da gashinta.


ya ce, “Iyayengijina, ina roƙonku ku ratse zuwa gidan baranku, ku kwana, ku wanke ƙafafunku, da sassafe kuma sai ku kama hanyarku.” Suka ce, “A'a, a titi za mu kwana.”


Sai ta rusuna har ƙasa, ta ce, “Ni baranyarsa ce, ina a shirye in wanke ƙafafun barorinsa.”


Aka sa abinci a gabansa domin ya ci, amma ya ce, “Ba zan ci ba, sai na faɗi abin da yake tafe da ni.” Laban ya ce, “Faɗi maganarka.”


Sa'ad da Laban ya sami labari a kan Yakubu ɗan 'yar'uwarsa, sai ya sheƙo ya tarye shi, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kawo shi a gidansa. Yakubu ya labarta wa Laban al'amura duka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ