Sa'an nan na yi ruku'u, na yi wa Ubangiji sujada, na yabi Ubangiji Allah na maigidana, Ibrahim, wanda ya bishe ni a hanya sosai, in auro wa ɗansa 'yar danginsa.
Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra'ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba’ ” Sai jama'ar suka durƙusa suka yi sujada.
Sai Ezra ya yabi Ubangiji Allah Maɗaukaki. Jama'a duka suka amsa, “Amin, amin!” suna ɗaga hannuwansu. Suka sunkuyar da kansu har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada.
Sai sarki Hezekiya tare da sarakunansa, suka faɗa wa Lawiyawa su yi ta raira yabo ga Ubangiji da kalmomin Dawuda, da na Asaf maigani. Da murna suka raira yabo, suka sunkuya suka yi sujada.
Sa'an nan Dawuda ya ce wa taro duka, “Sai ku yabi Ubangiji Allahnku yanzu.” Taron jama'a kuwa suka yabi Ubangiji Allah na kakanninsu, suka rusuna har ƙasa, suka yi wa Ubangiji sujada, suka kuma girmama sarki.
Da Gidiyon ya ji mafarkin, har da fassarar, sai ya yi sujada, ya koma a sansaninsu na Isra'ilawa. Da ya isa, sai ya ce, “Ku tashi, gama Ubangiji ya ba da rundunar Madayanawa a gare ku.”