Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 24:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Budurwa mai kyan tsari ce. Tana da kyan gani ƙwarai, budurwa ce, ba wanda ya taɓa saninta. Ta gangara zuwa rijiyar ta cika tulunta, ta hauro.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 24:16
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da mutanen wurin suka tambaye shi matarsa, ya ce, “Ita 'yar'uwata ce,” gama yana jin tsoro ya ce, “Ita matata ce,” don kada mutanen wurin su kashe shi saboda Rifkatu, da yake ita kyakkyawa ce.


Ina barci, amma zuciyata na a farke, Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata, Wadda ba wanda zai kushe ki. Kaina ya jiƙe da raɓa, Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.


Ya bar dukan abin da yake da shi a hannun Yusufu. Tun da ya same shi, ba ruwansa da kome, sai dai abincin da zai ci. Yusufu fa kyakkyawa ne mai kyan gani.


Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa'u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.”


Sa'ad da yake gab da shiga Masar, ya ce wa matarsa, Saraya, “Na sani ke kyakkyawar mace ce,


Lai'atu dai ba kyakkyawa ba ce, amma Rahila kyakkyawa ce, dirarriya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ