Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 24:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Sai bawan ya ɗibi raƙuma goma na maigidansa ya tafi, ɗauke da kowane irin abubuwa masu kyau daga wurin maigidansa. Ya fita don yă tafi Aram-Naharayim, ya kama hanyarsa zuwa garin Nahor.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 24:10
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin ba su zo sun tarye ku, su kawo muku abinci da ruwa ba sa'ad da kuke a hanyarku, lokacin da kuka fito daga Masar. Ga shi kuma, sun yi ijara da Bal'amu ɗan Beyor daga Fetor ta Mesofatamiya ya zo ya la'anta ku.


Sai Tera ya ɗauki ɗansa Abram da Lutu ɗan Haran, jikansa, da Saraya surukarsa, wato matar ɗansa Abram, suka tafi tare, daga Ur ta Kalidiyawa zuwa ƙasar Kan'ana, amma da suka isa Haran, suka zauna a can.


Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya,


Sa'ad da Ammonawa suka ga sun mai da kansu abin ƙi ga Dawuda, sai Hanun da Ammonawa suka aika da talanti dubu (1,000) na azurfa don su yi ijara da karusai da mahayan dawakai daga Mesofotamiya, da jihohin Ma'aka ta Suriya, da Zoba.


Yakubu kuwa ya ci gaba da tafiyarsa, har ya kai ƙasar Mesofotamiya.


Domin haka, ɗana, ka ji muryata, ka tashi ka gudu zuwa wurin Laban ɗan'uwana a Haran,


Ibrahim ya ce wa baransa, daɗaɗɗen gidansa wanda yake hukunta dukan abin da yake da shi, “Sa hannunka a ƙarƙashin cinyata,


Da Abram da Nahor suka yi aure, sunan matar Abram Saraya, sunan matar Nahor kuwa Milka, ita 'yar Haran ce, mahaifin Milka da Iskaya.


Kwanakin Tera shekara ce metan da biyar, Tera kuwa ya rasu a Haran.


Sa'ad da raƙuman suka gama sha, mutumin ya ɗauki zoben zinariya mai nauyin rabin shekel, ya sa mata a hanci. Ya kuma ɗauki mundaye biyu na shekel goma na zinariya ya sa a hannuwanta,


Sai baran ya kawo kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, ya bai wa Rifkatu, ya kuma ba ɗan'uwanta da mahaifiyarta kayan ado masu tsada.


Da ya duba haka sai ya ga rijiya cikin saura, ga kuwa garken tumaki uku suna daura da ita, gama daga cikin rijiyar nan ake shayar da garkunan. Murfin rijiyar, dutse ne, babba.


Sa'ad da Tera ya yi shekara saba'in, ya haifi Abram, da Nahor, da Haran.


Ana nan bayan waɗannan al'amura, aka faɗa wa Ibrahim, “Ga shi, Milka ta haifa wa ɗan'uwanka Nahor, 'ya'ya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ