Mala'ikun nan biyu kuwa suka isa Saduma da maraice, Lutu kuwa yana zaune a ƙofar Saduma. Sa'ad da Lutu ya gan su sai ya miƙe ya tarye su. Sai ya yi ruku'u a gabansu.
Da ya ɗaga idonsa, ya duba sai ga mutum uku suna tsaye a gabansa. Da ya gan su, sai ya sheƙa da gudu daga ƙofar alfarwar, don ya tarye su. Ya yi ruku'u,
“Ka ji mu, ya shugaba, gama kai yardajjen Allah ne a tsakaninmu. Ka binne matarka a kabari mafi kyau na kaburburanmu, ba waninmu da zai hana maka kabarinsa, ko ya hana ka ka binne matarka.”