Dawuda ya ce wa Ahimelek Bahitte, da Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab, “Wa zai tafi tare da ni zuwa sansanin Saul?” Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”
a cikin kogon da yake a Makfela, gabashin Mamre, a ƙasar Kan'ana, wanda Ibrahim ya saya duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.
Rifkatu kuwa ta ce wa Ishaku, “Na gaji da raina saboda matan Hittiyawa. Idan Yakubu zai auri ɗaya daga cikin waɗannan mata na Hittiyawa, wato daga matan ƙasar, wane amfani raina zai daɗa mini?”