Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 23:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Ibrahim ya yarda da Efron. Ibrahim kuwa ya auna wa Efron yawan shekel da ya ambata a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu bisa ga nauyin da 'yan kasuwa suke amfani da shi a wancan lokaci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Ibrahim ya yarda da sharuɗan Efron, sai ya auna masa farashin da ya faɗa a kunnuwan Hittiyawa, shekel ɗari huɗu na azurfa, bisa ga ma’aunin da ’yan kasuwa suke amfani da shi a lokacin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 23:16
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai na ce musu, “Idan kun ga daidai ne sai ku biya ni hakkina, idan kuwa ba haka ba ne, to, ku riƙe abinku!” Sai suka biya ni tsabar azurfa talatin, ladana.


Sai na sayi gonar a Anatot daga hannun Hanamel ɗan kawuna, na biya shi shekel goma sha bakwai na azurfa.


A cikin wannan al'amari kuwa kada kowa ya keta haddi, har ya cuci ɗan'uwansa, domin Ubangiji mai sakamako ne a kan dukkan waɗannan abubuwa, kamar yadda muka gargaɗe ku, muka tabbatar muku tun da wuri.


Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin ƙauna, ko mene ne daɗɗaɗar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani.


Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari'a ke nan.


Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”


“Shekel zai zama gera ashirin. Mainanku ɗaya zai zama shekel sittin.”


Ba za a saye ta da zinariya tsantsa ba. Azurfa ba za ta iya biyan tamaninta ba.


Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji.


amma da muka isa zango muka buɗe tayakanmu sai ga kuɗin kowannenmu cif cif bakin taikinsa, don haka ga su a hannunmu, mun sāke komowa da su,


“Ya shugabana, ka ji ni, don ɗan yankin ƙasa na shekel ɗari huɗu, a bakin me yake, a tsakaninmu? Binne matarka.”


Sai aka ɗebo su aka mai da su Shekem, aka sa su a kabarin da Ibrahim ya saya da kuɗi azurfa a wurin 'ya'yan Hamor a nan Shekem.


Yakubu ya umarce su, ya ce musu, “Ga shi, lokacin mutuwa ya gabato da za a kai ni wurin jama'ata da suka riga ni. Sai ku binne ni tare da kakannina a cikin kogon da yake a saurar Efron Bahitte,


gama 'ya'yansa suka ɗauke shi zuwa ƙasar Kan'ana, suka kuwa binne shi a kogon da yake saurar Makfela a gabashin Mamre, wanda Ibrahim ya saya, duk da saurar, daga wurin Efron Bahitte, ya zama mallakarsa don makabarta.


Sa'ad da ya yi aski yakan auna nauyin gashin kansa, nauyin yakan kai wajen shekel ɗari biyu. Gama a ƙarshen kowace shekara yake aski, sa'ad da gashin ya yi masa nauyi.


Na sa hannu a takarda, na buga hatimi na liƙe, na sami shaidu na kuwa auna kuɗin da ma'auni.


Amma sarki ya ce wa Arauna, “A'a, saye zan yi daga gare ka da tamani. Ba zan miƙa wa Ubangiji Allahna hadayun ƙonawa da abin da ban yi wahalarsa ba.” Dawuda ya sayi masussukar da shanu a bakin shekel hamsin na azurfa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ