Sai Ibrahim ya yi ruku'u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, “Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa'in ta haifi ɗa?”
Ishaku kuwa ya shiga da ita cikin alfarwarsa ya ɗauki Rifkatu ta zama matarsa, ya kuwa ƙaunace ta. Ta haka Ishaku ya ta'azantu bayan rasuwar mahaifiyarsa.