Sai Elihu, ɗan Barakel, mutumin Buz, daga cikin iyalin Arama, ya husata, yana fushi da Ayuba saboda ya baratar da kansa, bai bari Allah ya baratar da shi ba.
Bal'amu kuwa ya faɗi jawabinsa, ya ce “Tun daga Aram Balak ya kawo ni, Shi Sarkin Mowab ne daga gabashin duwatsu. ‘Zo, la'anta mini Yakubu, Zo, ka tsine wa Isra'ila!’
Baran ya ɗibi raƙuma goma daga cikin raƙuman maigidansa. Ya tashi, yana ɗauke da tsaraba ta kowane irin abu mai kyau na maigidansa a hannunsa. Ya kama hanyar Mesofotamiya zuwa birnin Nahor.