Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 22:17 - Littafi Mai Tsarki

17 hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 tabbatacce zan albarkace ka, zan kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar taurari a sararin sama, kamar kuma yashi a bakin teku. Zuriyarka za su mallaki biranen abokan gābansu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 22:17
50 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Ubangiji ya fito da shi waje ya ce, “Ina so ka dubi sararin sama, ka kuma ƙidaya taurari, in kana iya ƙidaya su.” Sai kuma ya ce masa, “Haka zuriyarka za ta zama.”


Kamar yadda ba a iya ƙidaya rundunan sammai ba, ba a iya kuma auna yashin teku ba, haka nan zan yawaita zuriyar bawana Dawuda da Lawiyawa, firistoci, masu yi mini hidima.”


Zan mai da zuriyarka kamar turɓayar ƙasa, har in mutum ya iya ƙidaya turɓayar ƙasa, to, a iya ƙidaya zuriyarka.


Zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sararin sama, zan kuwa ba zuriyarka dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin zuriyarka kuma al'umman duniya duka za su sami albarka,


Suka sa wa Rifkatu albarka, suka ce mata, “'Yar'uwarmu, ki zama mahaifiyar dubbai, Har dubbai goma, Bari zuriyarki kuma su gāji ƙofofin maƙiyansu!”


Sa'an nan mala'ika na bakwai ya busa ƙahonsa, sai aka ji waɗansu muryoyi masu ƙara a Sama, suna cewa, “Mulkin duniya ya zama mulkin Ubangijinmu da na Almasihunsa, shi kuma zai yi mulki har abada abadin.”


Yabo yā tabbata ga Allahn Ubangijinmu Yesu Almasihu, da Ubansa kuma, wanda ya yi mana albarka da kowace albarka ta Ruhu, basamaniya, a cikin Almasihu,


gama Ubangiji ya riɓaɓɓanya ku, har yawanku ya kai kamar taurarin sama.


Gama ka riga ka ce, ‘Zan yi maka alheri, in kuma sa zuriyarka su yi yawa kamar yashin teku, waɗanda ba su lasaftuwa saboda yawansu.’ ”


Godiya tā tabbata ga Allah wanda yake ba mu nasara ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Ka kuwa ba su wannan ƙasa wadda ka rantse za ka ba kakanninsu. Ƙasar da take cike da yalwar albarka.


Gama raunin Samariya, ba ya warkuwa, Gama ya kai Yahuza, Ya kuma kai ƙofar jama'ata a Urushalima.”


Sarki Sulemanu kuma ya yi jiragen ruwa a Eziyon-geber wadda take kusa da Elat, a bakin Bahar Maliya a ƙasar Edom.


sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su kama shi, su kawo shi wurin dattawan garin a dandalin ƙofar gari.


Allah Maɗaukaki ya sa maka albarka, ya sa ka hayayyafa ya riɓaɓɓanya ka, ka zama ƙungiyar jama'o'i,


Zan arzuta ka ainun, daga gare ka zan yi al'ummai, daga gare ka kuma sarakuna za su fito.


Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.


Alkawarin nan da aka yi wa Ibrahim da zuriyarsa, cewa zai zama magājin duniya, ba ta Shari'a aka yi masa ba, amma domin ya ba da gaskiya ne, shi ya sa Allah ya karɓe shi mai adalci ne.


A game da Isra'ila Ishaya ma ya ɗaga murya ya ce, “Ko da yake yawan Isra'ilawa ya kai kamar yashin teku, duk da haka kaɗan ne za su sami ceto.


ya ce, “Hakika zan yi maka albarka, in kuma riɓanya zuriyarka.”


Saboda haka, daga mutum ɗaya, wanda dā shi ma da matacce kusan ɗaya ne, aka haifi zuriya masu yawa kamar taurari, kamar yashi kuma dangam a bakin teku.


Bayan rasuwa Ibrahim, Allah ya sa wa Ishaku ɗansa albarka. Ishaku kuwa ya zauna a Biyer-lahai-royi.


Da daren nan Ubangiji ya bayyana gare shi ya ce, “Ni ne Allah na mahaifinka, kada ka ji tsoro, gama ina tare da kai, zan sa maka albarka in riɓaɓɓanya zuriyarka saboda bawana Ibrahim.”


ya kuma sa ka sami albarkar Ibrahim da zuriyarka tare da kai, har da za ka amshe ƙasar baƙuncinka wadda Allah ya bai wa Ibrahim!”


Kakanninku saba'in ne suka gangara zuwa Masar, amma yanzu Ubangiji Allahnku ya riɓaɓɓanya ku, kuka yi yawa kamar taurarin sama.”


Kada ku ɗauka daga cikin abin da aka haramta don zafin fushin Ubangiji ya huce, ya yi muku jinƙai, ya ji tausayinku, ya kuma riɓaɓɓanya ku ma kamar yadda ya rantse wa kakanninku,


Sarki Dawuda bai ƙidaya waɗanda shekarunsu suka kasa ashirin ba, gama Ubangiji ya yi alkawari zai sa mutanen Isra'ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.


Yanzu fa ya Ubangiji Allah, alkawarin da ka yi wa tsohona ya cika, gama ka naɗa ni sarki a kan jama'a mai yawa kamar turɓaya.


“Duk da haka yawan mutanen Isra'ila Zai zama kamar yashi a bakin teku, Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba. Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’


Ya yi zango a nan a wannan dare, ya kuwa bai wa ɗan'uwansa Isuwa kyauta daga cikin abin da yake da shi,


Ka tuna da bayinka Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, waɗanda kai da kanka ka rantse musu, ka ce, ‘Zan riɓaɓɓanya zuriyarku kamar taurarin sama, in kuma ba ku wannan ƙasa duka da na alkawarta zan bayar ga zuriyarku. Za su kuwa gāje ta har abada’ ”


Ubangiji Allah na kakanninku ya riɓa yawanku har sau dubu, ya sa muku albarka yadda ya alkawarta muku!


in dai za ku yi wa Ubangiji Allahnku biyayya, ku kiyaye dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, ku kuma ku aikata abin da yake daidai ga Ubangiji Allahnku.”


Shawarata ita ce a tattara maka dukan Isra'ilawa tun daga Dan har zuwa Biyer-sheba, yawansu kamar yashi a bakin teku. Kai kuma da kanka ka tafi wurin yaƙin.


Mutanen Yahuza da na Isra'ila suka yi yawa kamar yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka yi murna.


Ka riɓaɓɓanya zuriyarsu kamar taurarin sararin sama, Ka sa suka ci ƙasar, suka zauna cikinta, Ƙasar da aka yi wa kakanninsu alkawari za ka ba su.


Zuriyarku za su yi yawa kamar tsabar yashi, Zan kuma tabbatar, cewa ba za a hallaka su ba.”


“Ka ce wa 'yan'uwanka maza, ‘Ku mutanena ne,’ ka kuma ce wa 'yar'uwarka, ‘Kin sami jinƙai!’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ