Mala'ikan da ya fanshe ni Daga dukan mugunta, Ya sa wa samarin albarka, Bari a dinga ambatarsu da sunana, Da sunan Ibrahim da na Ishaku iyayena, Bari kuma su riɓaɓɓanya, su zama taron jama'a a tsakiyar duniya.”
A can mala'ikan Ubangiji ya bayyana gare shi cikin harshen wuta daga cikin kurmi. Da Musa ya duba, sai ga kurmin yana cin wuta, amma duk da haka bai ƙone ba.
Baƙon ya ce, “Na yi maka alkawari matarka Saratu za ta haifi ɗa a wata na tara nan gaba. Zan sāke zuwa a lokacin.” Saratu kuwa tana ƙofar alfarwa, a bayansu, tana kasa kunne.
Abin da na faɗa gaskiya ne, Ba kuwa zai sāke ba. Ni, a dukkan yadda nake, na yi alkawari mai ƙarfi, Kowa da kowa zai zo ya durƙusa a gabana, Ya yi wa'adin zama mai biyayya a gare ni.
A ranar, Ubangiji zai kiyaye mazaunan Urushalima, har wanda yake marar ƙarfi a cikinsu zai zama mai ƙarfi kamar Dawuda. Jama'ar Dawuda za ta zama kamar Allah, kamar mala'ikan Ubangiji a gabansu.