Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 21:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ta kuma ce, “Dā wa zai iya ce wa Ibrahim Saratu za ta bai wa 'ya'ya mama? Duk da haka cikin tsufansa na haifa masa ɗa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ta kuma ƙara da cewa, “Dā, wa zai iya ce wa Ibrahim, Saratu za tă yi renon yara? Duk da haka na haifar masa ɗa cikin tsufansa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 21:7
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ko akwai wanda ya taɓa gani ko ya ji labari irin wannan abu? Ko an taɓa haihuwar al'umma rana ɗaya? Sihiyona ba za ta sha wahala ba kafin a haifi al'umma.


wato, a lokacin da ya dawo, tsarkakansa su ɗaukaka shi, duk masu ba da gaskiya kuma su yi al'ajabinsa a ranar nan, don kun gaskata shaidar da muka yi muku.


An yi wannan ne kuwa domin a yanzu a sanar da hikimar Allah iri iri ga manyan mala'iku da masu iko a samaniya, ta hanyar Ikkilisiya.


Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu, Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra'ilawa. Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra'ilawa!’


Gama kai kaɗai ne Maɗaukaki, ya Allah, Kai kaɗai ne ka aikata abubuwa na banmamaki.


Ba wani allah kamarka, ya Ubangiji, Ba ko ɗaya, ba wanda zai iya aikata abin da kake aikatawa.


Sa'an nan za ki ce wa kanki, ‘Wa ya haifa mini waɗannan 'ya'ya? Na rasa 'ya'yana, ba kuwa zan iya haifar waɗansu ba. Aka kore ni, aka yi mini ɗaurin talala, Wane ne ya haifi waɗannan 'ya'ya? Aka bar ni, ni kaɗai, Daga ina waɗannan 'ya'ya suka fito?’ ”


Sai Ibrahim ya yi ruku'u, ya yi dariya a zuciyarsa, ya ce wa kansa, “Za a haifa wa mai shekara ɗari ɗa? Zai yiwu Saratu mai shekara tasa'in ta haifi ɗa?”


Ubangiji ya ce wa Ibrahim, “Me ya ba Saratu dariya, har da ta ce, ‘Ashe zan haifi ɗa, a yanzu da na riga na tsufa?’


Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.


La'ananne ne mutum da ya kai wa mahaifina labari Cewa, “An haifa maka ɗa,” don ya sa shi farin ciki.


Sa'ad da na tashi da safe don in ba ɗana mama, sai ga shi, matacce. Da na duba sosai, sai na ga ba nawa ba ne, wanda na haifa.”


Ita kuwa ta haifa masa ɗa, Genubat, wanda Tafenes ta yi renonsa a gidan Fir'auna. Genubat kuwa ya zauna tare da 'ya'yan Fir'auna, maza.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ