Waɗannan duka sun mutu cikin bangaskiyarsu, ba su kuwa sami abubuwan da aka yi musu alkawari ba, amma da suka tsinkato su, sai suka yi ta murna da ganinsu, suna kuma yarda su baƙi ne, bare kuma a duniya.
Ta wurin bangaskiya kuma ya yi baƙunci a ƙasar alkawari, kamar dai a ƙasar bare, suna zaune a cikin alfarwai, shi da Ishaku da Yakubu, abokan tarayya ga gādon alkawarin nan.
“Ka ji addu'ata, ya Ubangiji, Ka kuma kasa kunne ga roƙona, Kada ka yi shiru sa'ad da na yi kuka gare ka! Yadda dukan kakannina suka yi, Ni baƙonka ne na ɗan lokaci.