Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 21:22 - Littafi Mai Tsarki

22 A lokacin nan fa, ya zamana Abimelek, da Fikol shugaban sojojinsa ya zo ya ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai cikin sha'aninka duka,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 A lokacin nan Abimelek da Fikol, komandan rundunoninsa suka zo suka ce wa Ibrahim, “Allah yana tare da kai a ko mene ne kake yi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 21:22
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Abimelek ya zo daga Gerar tare da Ahuzat mashawarcinsa da Fikol shugaban sojojinsa, don ya ga Ishaku.


Ubangiji kuwa ya ce wa Joshuwa, “A yau ɗin nan zan fara ɗaukaka ka a gaban dukan Isra'ilawa domin su sani, kamar yadda na kasance tare da Musa, haka kuwa zan kasance tare da kai.


Suka ce, “Lalle, mun gani a fili Ubangiji yana tare da kai, saboda haka muke cewa bari rantsuwa ta kasance tsakaninmu da kai, bari kuma mu ƙulla alkawari da kai,


ya ce, matarsa Saratu 'yar'uwarsa ce. Sai Abimelek Sarkin Gerar ya aika, aka ɗauko masa Saratu.


Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kansa ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.”


asiran zuciyarsa kuma su tonu. Ta haka sai ya fāɗi ya yi wa Allah sujada, yana cewa lalle Allah na cikinku.


To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?


Ku yi ta shirye-shiryenku! Amma ko kusa ba za ku yi nasara ba. Ku yi magana a kan dukan abin da kuke so! Amma duk a banza, gama Allah yana tare da mu.


To, ga shi, zan sa su waɗanda suke daga jama'ar Shaiɗan, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, ƙarya suke yi, zan sa su, su zo, su kwanta a gabanka, su sani dai na ƙaunace ka.


“Ga shi, budurwa za ta yi juna biyu, ta haifi ɗa, Za a kuma sa masa suna Immanuwel.” (Ma'anar Immanuwel kuwa itace Allah na tare da mu.)


Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, a waɗannan kwanaki mutum goma daga kowace al'umma da kowane harshe za su kama kafa wurin Bayahude, su ce, ‘Ka yardar mana mu tafi tare da kai, gama mun ji Allah yana tare da ku.’ ”


Ubangiji ya ce wa Isra'ila, “Dukiyar Masar da ta Habasha za ta zama taku, Dogayen mutanen Seba kuma za su zama bayinku, Za su bi ku suna a ɗaure da sarƙoƙi. Za su rusuna a gabanku su tuba, su ce, ‘Allah yana tare da ku, shi kaɗai ne Allah.’ ”


Sulemanu ɗan Dawuda ya kahu sosai cikin mulkinsa, gama Ubangiji Allahnsa yana tare da shi, Ubangiji kuwa ya sa shi ya zama mashahuri.


Amma Laban ya ce masa, “Da za ka yarda mini, sai in ce, na fahimta bisa ga istihara, cewa Ubangiji ya sa mini albarka saboda kai.


Ibrahim ya yi addu'a ga Allah, Allah kuwa ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata, har kuma suka sami haihuwa.


Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”


Abimelek ya ɗauki tumaki da takarkarai, da bayi mata da maza, ya ba Ibrahim, ya kuma mayar masa da matarsa Saratu.


ya ce musu, “Na ga ba ni da sauran farin jini wurin mahaifinku kamar dā. Amma Allah na mahaifina yana tare da ni.


Sama'ila fa ya yi girma, Ubangiji yana tare da shi. Dukan maganarsa kuwa Ubangiji yana cika ta.


Suka tafi kagarar Taya da dukan garuruwan Hiwiyawa, da na Ƙan'aniyawa. Daga can suka tafi ƙasar kudu ta Yahuza a Biyer-sheba.


Dawuda kuwa ya yi wa Saul alkawari. Sa'an nan Saul ya koma gida, amma Dawuda da mutanensa suka koma wurin ɓuya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ