Ga zancen Isma'ilu kuwa, na ji, ga shi, zan sa masa albarka in kuma riɓaɓɓanya shi ainun. Zai zama mahaifin 'ya'yan sarakuna goma sha biyu, zan maishe shi al'umma mai girma.
Ibrahim ya tashi da sassafe, ya kuma ɗauki gurasa da salkar ruwa, ya bai wa Hajaratu, ya ɗora kafaɗarta. Sai ya ba ta ɗanta, ya sallame ta. Ta tafi ta yi ta yawo cikin jejin Biyer-sheba.