Ai, kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙin ciki, ba na farin ciki ba. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.
Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.
Sai zuciyar sarki ta tsinke, ya hau cikin ɗakin da yake kan garun ƙofar garin yana ta kuka, yana cewa, “Ya ɗana Absalom, ɗana! Wayyo, ɗana Absalom! Da ma ni ne na mutu, ba kai ba. Ya Absalom, ɗana, ɗana!”
Amma Allah ya ce wa Ibrahim, “Kada zuciyarka ta ɓaci saboda yaron da kuma baiwarka. Kome Saratu ta faɗa maka, ka yi yadda ta ce, gama ta wurin Ishaku za a riƙa kiran zuriyarka.