Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 20:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Amma Allah ya zo wurin Abimelek cikin mafarki da dad dare ya ce masa, “Mutuwa za ka yi saboda matar da ka ɗauko, gama ita matar wani ce.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Amma wata rana da dad dare Allah ya zo wa Abimelek a cikin mafarki ya ce masa, “Kai da matacce ɗaya kuke, saboda matar da ka ɗauka. Ita matar aure ce.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 20:3
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Banda haka kuma, a lokacin da yake zaune a kan gadon shari'a, sai mata tasa ta aiko masa da cewa, “Ka fita daga sha'anin mara laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai a mafarkinsa.”


Yanzu fa, sai ka mayar wa mutumin da matarsa, gama shi annabi ne, zai yi maka addu'a, za ka kuwa rayu. In kuwa ba ka mayar da ita ba, ka sani hakika za ka mutu, kai, da dukan abin da yake naka.”


Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba, Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.


Yakan sanar a mafarkai ko a wahayi Sa'ad da barci mai nauyi ya ɗauke su, A sa'ad da suke barci a gadajensu.


Amma tun yana cikin wannan tunani, sai ga wani mala'ikan Ubangiji ya bayyana a gare shi a mafarki, ya ce, “Yusufu ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukar Maryamu matarka, domin cikin nan nata daga Ruhu Mai Tsarki ne.


Ya yi mafarki, ga wani tsani tsaye daga ƙasa, kansa ya kai sama, sai ga mala'ikun Allah suna hawa da sauka ta kansa!


Sai Yunusa ya kama tafiya yana ratsa birnin, da ya yi tafiyar yini guda, sai ya yi shela ya ce, “Nan da kwana arba'in za a hallaka Nineba.”


Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.” Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”


Shi kuwa sai ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa 'yan'uwansa, ya ce, “Ga shi kuma na sāke yin wani mafarki, na ga rana, da wata, da taurari goma sha ɗaya suna sunkuya mini.”


Yusufu ya yi mafarki. Sa'ad da ya faɗa wa 'yan'uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.


Amma Allah ya zo wurin Laban Ba'aramiye cikin mafarki da dad dare, ya ce masa, “Ka kula fa, kada ka ce wa Yakubu kome, ko nagari ko mugu.”


Sai Ubangiji ya wahalar da Fir'auna da gidansa da manya manyan annobai saboda matar Abram, Saraya.


Sai Fir'auna ya kirawo Abram, ya ce, “Mene ne wannan da ka yi mini? Don me ba ka faɗa mini ita matarka ce ba?


Allah kuwa ya zo wurin Bal'amu ya ce masa, “Suwane ne mutanen da suke tare da kai?”


Amma bai yarda kowa ya zalunce su ba, Ya tsauta wa sarakuna da yawa saboda su.


Suka yi mafarki, su biyu ɗin, a dare ɗaya, da shi mai shayarwar da mai tuyar na gidan Sarkin Masar, waɗanda aka sa a kurkuku, kowanne kuwa da nasa mafarkin da kuma tasa irin fassarar mafarkin.


Sai Allah ya yi magana cikin wahayin dare, ya ce, “Yakubu.” Ya amsa ya ce, “Na'am.”


Domin ya kawar da su daga aikin da suke yi, Ya kuma kawar musu da girmankai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ