Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 20:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi zuwa wajen karkarar Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. A lokacin da Ibrahim yake baƙunci a Gerar,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi wajajen Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. Ya zauna a Gerar na ɗan lokaci,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 20:1
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Aka sāke yin yunwa a ƙasar, banda wadda aka yi a zamanin Ibrahim. Sai Ishaku ya tafi Gerar wurin Abimelek, Sarkin Filistiyawa.


Muryarsa ta sa hamada ta girgiza, Ta girgiza hamadar Kadesh.


Ubangiji kuwa ya bayyana ga Ibrahim kusa da itatuwan oak na Mamre, a lokacin da yake zaune a ƙofar alfarwarsa da tsakar rana.


Saul ya ci Amalekawa, tun daga Hawila har zuwa Shur, da yake gabashin Masar,


Gama ba ku amince da ni ba a gaban mutanen Isra'ila a wurin ruwan Meriba ta Kadesh a jejin Zin a wannan lokaci, domin ba ku nuna tsarkina a gaban jama'ar Isra'ila ba.


“Sai muka tashi daga Horeb, muka ratsa babban jejin nan mai bantsoro wanda kuka gani a hanyarmu zuwa ƙasar tuddai ta Amoriyawa, kamar yadda Ubangiji Allahnmu ya umarce mu, muka zo Kadesh-barneya.


Sa'ad da muka yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya aiko mala'ikansa, ya fisshe mu daga Masar. Ga mu nan a Kadesh, garin da yake kan iyakar ƙasarka.


Suka zo wurin Musa, da Haruna, da dukan taron jama'ar Isra'ila a jejin Faran a Kadesh. Suka faɗa musu labarin tafiyarsu, suka kuma nuna musu amfanin ƙasar da suka kawo.


Abimelek ya zo daga Gerar tare da Ahuzat mashawarcinsa da Fikol shugaban sojojinsa, don ya ga Ishaku.


Makiyayan Gerar kuwa suka yi faɗa da makiyayan Ishaku, suna cewa, “Ruwan namu ne.” Saboda haka Ishaku ya sa wa rijiyar suna Esek, domin sun yi jayayya a kanta.


A lokacin kuwa Ishaku ya riga ya zo daga Biyer-lahai-royi yana zaune a Negeb.


Domin haka Abram ya bar Masar zuwa Negeb, shi da matarsa, da abin da yake da shi duka tare da Lutu.


Yankin ƙasar Kan'aniyawa kuwa ya milla tun daga Sidon, har zuwa wajen Gerar, har zuwa Gaza, zuwa wajen Saduma, da Gwamrata, da Adma, da Zeboyim, har zuwa Lasha.


Domin haka aka kira sunan rijiyar, Biyer-lahai-royi, tana nan tsakanin Kadesh da Bered.


Mala'ikan Ubangiji kuwa ya sami Hajaratu a gefen wata maɓuɓɓugar ruwa a jeji, wato maɓuɓɓugar da take kan hanyar Shur.


Saraya matar Abram ba ta taɓa haihuwa ba, amma tana da baranya Bamasariya, sunanta Hajaratu.


Sai suka juya suka je Enmishfat, wato Kadesh, suka kuwa cinye ƙasar Amalekawa da kuma ta Amoriyawa waɗanda suka zauna cikin Hazazontamar.


Abram kuwa ya ci gaba da tafiya, ya nufi zuwa wajen Negeb.


Mazauninsa a tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake ɗaura da Masar wajen Assuriya. Suka ware daga danginsu suka yi zamansu.


Musa kuwa ya bi da Isra'ilawa daga Bahar Maliya, suka shiga jejin Sur. Suka yi tafiya kwana uku cikin jejin, ba su sami ruwa ba.


Ibrahim kuwa ya daɗe yana baƙunci a ƙasar Filistiyawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ