Ranar za ta zama dawwamammiyar shaida tsakanina da Isra'ilawa, cewa a kwana shida ni Ubangiji na yi sama da ƙasa, amma a rana ta bakwai na ajiye aiki, na huta’ ”
Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.
Ubangiji ne ya halicci sammai, Shi ne wanda yake Allah! Shi ne ya shata duniya ya kuma yi ta, Ya kafa ta, ta kahu da ƙarfi, za ta yi ƙarƙo! Bai halicce ta hamada da ba kome a ciki ba, Amma wurin zaman mutane. Shi ne wanda ya ce, “Ni ne Ubangiji, Ba kuwa wani Allah, sai ni.
Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su, Ya yi duniya, da dukan masu rai nata, Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta. Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,
Sa'an nan ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.
Sa'an nan suka yi wannan addu'a, suka ce, “Kai kaɗai ne Ubangiji, ya Ubangiji, Kai ne ka yi samaniya da taurari da sararin sama. Kai ne ka yi ƙasa, da teku, da kowane abu da yake cikinsu, Ka ba dukansu rai, Ikokin samaniya sun rusuna suna maka sujada.
Hiram ya ci gaba da cewa, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya yi sama da ƙasa, ya ba sarki Dawuda ɗa mai hikima, mai hankali, mai ganewa, wanda zai gina Haikali dominsa, ya gina fāda kuma domin kansa.
Mu kuwa da muka ba da gaskiya, muna shiga inuwar, yadda ya ce, “Sai na yi rantsuwa da fushina, na ce, ‘ba za su shiga inuwata ba sam,’ ” ko da yake ayyukan Allah gamammu ne tun daga farkon duniya.
Su kuwa da jin haka, sai suka ɗaga muryarsu ga Allah da nufi ɗaya, suka ce, “Ya Mamallaki, Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu,
Dantsena ne ya kafa harsashin ginin duniya, Ya kuma shimfiɗa sammai. Lokacin da na kira duniya da sararin sama, Sukan zo nan da nan, su gabatar da kansu!
Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.
Za a shimfiɗa su a rana, da a farin wata, da a gaban dukan rundunan sama, waɗanda suka ƙaunata, suka bauta wa, waɗanda suka nemi shawararsu, suka yi musu sujada. Ba za a tattara su a binne ba, amma za su zama juji a bisa ƙasa.
Saboda haka Allah ya juya musu baya, ya sallame su ga bautar taurari, yadda yake a rubuce a littafin annabawa cewa, “ ‘Ya ku jama'ar Isra'ila, Ni ne kuka yanka wa dabbobi, kuka miƙa wa hadaya, Har shekara arba'in a cikin jeji?
Za a murtsuke rana, da wata, da taurari su zama ƙura. Sararin sama zai shuɗe kamar yadda ake naɗe littafi, taurari kuma su faɗo kamar yadda ganyaye suke karkaɗewa daga itacen inabi ko na ɓaure.