Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 19:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Ga shi, ina da 'ya'ya mata biyu waɗanda ba su san namiji ba, bari in fito muku da su waje, ku yi yadda kuka ga dama da su, sai dai kada ku taɓa mutanen nan ko kaɗan, gama sun shiga ƙarƙashin inuwata.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Duba, ina da ’ya’ya mata biyu waɗanda ba su taɓa sanin namiji ba, bari in kawo muku su ku yi kome da kuke so da su. Amma kada ku taɓa waɗannan mutane, gama su baƙina ne kuma dole in tsare su.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 19:8
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga 'yata budurwa da ƙwarƙwararsa, bari in fito muku da su, ku yi abin da kuka ga dama da su, amma kada ku yi wa mutumin nan wannan abin kunya!”


In haka ne, ba sai mu yi ta yin mugun aiki don ya zama sanadin nagarta ba? Kamar yadda dai waɗansu suke mana yanke, cewa haka muke faɗa. Hukuncin da za a yi wa irin waɗannan kuwa daidai ne.


Ya rasa abin da zai faɗa ne, don sun tsorata da gaske.


Ku ci abincinku tare da mayunwata, ku kuma shigo da matalauta, marasa mahalli a cikin gidajenku. Idan kuma kun ga wanda yake tsirara, ku sa masa sutura, kada kuma ku ɓoye fuskokinku ga 'yan'uwanku.


Itacen ƙaya kuwa ya ce wa itatuwan, ‘In da gaske kuke, kuna so ku naɗa ni sarkinku, to, sai ku zo, ku fake a inuwata, in ba haka ba kuwa, bari wuta ta fito daga itacen ƙaya ta cinye itacen al'ul na Lebanon.’ ”


Haruna kuwa ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, kada ka ji haushina, ka san jama'an nan sarai da irin halinsu na son aikata mugunta.


Ra'ubainu kuwa ya ce wa mahaifinsa, “Ka kashe 'ya'yana biyu maza idan ban komo da shi ba, ka sa shi a hannuna, zan kuwa komo maka da shi.”


ni kuwa in tafi in kawo ɗan abinci, don rayukanku su wartsake, bayan haka sai ku wuce, tun da yake kun biyo ta wurin baranku.” Sai suka ce, “Madalla! Ka aikata bisa ga faɗarka.”


ya ce, “Ina roƙonku 'yan'uwana, kada ku aikata mugunta haka.


Tsohon kuwa ya fito wurinsu, ya ce musu, “A'a, 'yan'uwana, kada ku yi mugun abu haka, wannan ya sauka a gidana, kada ku yi wannan rashin kunya.


Idan ka kwaɓi mai fāriya, za ka gamu da cin mutunci, idan ka tsauta wa mugu, kai ne za ka cutu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ