Sama'ila ya ce masa, “Kamar yadda takobinka ya mai da mata marasa 'ya'ya, haka za a mai da mahaifiyarka ta zama marar ɗa.” Sai Sama'ila ya sassare Agag gunduwa gunduwa a gaban bagade a Gilgal.
Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.
Ga shi, ina da 'ya'ya mata biyu waɗanda ba su san namiji ba, bari in fito muku da su waje, ku yi yadda kuka ga dama da su, sai dai kada ku taɓa mutanen nan ko kaɗan, gama sun shiga ƙarƙashin inuwata.”
Saboda haka suka sa shi ya bugu da ruwan inabi a wannan dare kuma, ƙaramar ta shiga ta kwana da shi. Shi kuwa bai san da kwanciyarta ba balle fa tashinta.
“Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Kada ku dami Mowabawa, ko kuwa ku tsokane su, gama ba zan ba ku ƙasarsu ku mallake ta ba. Na riga na bayar da Ar ta zama mallakar zuriyar Lutu.’ ”