Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 19:30 - Littafi Mai Tsarki

30 Lutu ya fita daga Zowar, ya zauna cikin tuddai da 'ya'yansa biyu mata, gama yana jin tsoro ya zauna a Zowar. Ya zauna a cikin kogo da 'ya'yansa biyu mata.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

30 Lot da ’ya’yansa biyu mata suka bar Zowar suka kuma zauna a cikin duwatsu, gama ya ji tsoro yă zauna a Zowar. Shi da ’ya’yansa biyu mata suka zauna a ciki wani kogo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 19:30
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

ga shi, baranka ya sami tagomashi a idonka, ka kuwa nuna mini babban alheri da ka ceci raina, amma ba zan iya in kai tuddan ba, kada hatsarin ya same ni a hanya, in mutu.


“Mutanen Heshbon da na Eleyale suna kururuwa ana iya jin kururuwansu a Yahaza. Ana iya jinta kuma a Zowar, da Horonayim, da Eglat-shelishiya. Har ma ruwan Nimra ya ƙafe.


Zuciyata ta yi kuka ainun saboda Mowab! Mutane sun gudu zuwa cikin garin Zowar. Waɗansu sun haura zuwa Luhit, suna tafe suna kuka, waɗansu sun tsere zuwa Horonayim, suna hargowa saboda baƙin ciki.


da Negeb, da filin kwarin Yariko, birnin itatuwan giginya, har zuwa Zowar.


Kamar ambaliyar ruwa mai fushi kake, Amma ba za ka zama mafi daraja ba, Domin ka hau gadon mahaifinka, Sa'an nan ka ƙazantar da shi.


Sa'ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko'ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”


Amma Abram ya ce wa Sarkin Saduma, “Na riga na rantse wa Ubangiji Allah Maɗaukaki, wanda ya yi sama da ƙasa,


Lutu ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, ga shi kuwa da dausayi mai kyau ƙwarai, sai ka ce gonar Ubangiji, kamar ƙasar Masar wajen Zowar, tun kafin Allah ya hallaka Saduma da Gwamrata.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ