Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 19:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka ratse suka shiga gidansa, ya shirya musu liyafa, ya toya musu abinci marar yisti, suka ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Amma ya nace musu ƙwarai, sai suka tafi tare da shi, suka kuma shiga gidansa. Ya shirya musu abinci, ya gasa burodi marasa yisti, suka ci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 19:3
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Matar kuwa ta yi hanzari ta yanka turkakken maraƙinta, ta ɗauki gari ta kwaɓa, ta toya abinci marar yisti da shi.


Gidiyon ya tafi gida, ya yanka ɗan akuya, ya dafa, ya yi waina marar yisti ta gāri mudu guda. Ya sa naman a kwandon, romon kuwa ya zuba a tukunya, ya kawo, ya miƙa masa a gindin itacen oak.


Kada ku daina yi wa baƙi alheri, gama ta haka ne waɗansu suka sauki mala'iku ba da sani ba.


Saboda haka, sai mu riƙa yin idinmu, ba da gurasa mai tsohon yisti ba, ba kuwa gauraye da yisti na ƙeta da na mugunta ba, sai dai da gurasa marar yisti ta sahihanci da ta gaskiya.


Suka toya abinci marar yisti da ƙullun da suka fita da shi daga Masar, gama ba su sa yisti cikin ƙullun ba domin an iza ƙyeyarsu, ba su sami damar dakatawa ba, ba su kuwa shirya wa kansu guzuri ba.


Ƙaunar Almasihu a gare mu, ita take mallakarmu, saboda haka mun tabbata, da yake wani ya mutu saboda dukan mutane, ashe kuwa, mutuwarsu ce dukansu.


Nan aka yi masa abincin dare, Marta ce ta yi hidima, Li'azaru kuwa yana cikin masu ci tare da shi.


Sai ubangijin biki ya ce wa bawan, ‘Fita, ka bi gwadabe-gwadabe da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana.


Ina gaya muku, ko da yake ba zai tashi ya ba shi wani abu don yana amininsa ba, amma saboda nacinsa zai tashi ya ba shi ko nawa yake bukata.


Sai Lawi ya yi masa ƙasaitacciyar liyafa a gidansa, akwai kuwa taron masu karɓar haraji da waɗansu mutane suna ci tare da su.


Wata rana Elisha ya wuce zuwa Shunem inda wata mace take da zama, sai ta gayyace shi cin abinci. Don haka duk lokacin da ya bi ta wannan hanya, sai ya ratsa ta gidanta, ya ci abinci.


“Za ku yi kwana bakwai kuna cin abinci marar yisti. A rana ta fari za ku fitar da yisti daga cikin gidajenku, gama duk wanda ya ci abin da aka sa wa yisti tun daga rana ta fari har zuwa ta bakwai za a fitar da shi daga cikin Isra'ila.


Yaron ya yi girma, aka yaye shi, Ibrahim kuwa ya yi babban biki a ranar da aka yaye Ishaku.


ya ce, “Iyayengijina, ina roƙonku ku ratse zuwa gidan baranku, ku kwana, ku wanke ƙafafunku, da sassafe kuma sai ku kama hanyarku.” Suka ce, “A'a, a titi za mu kwana.”


Ya ce masa, “Shigo, ya mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”


Sai ya shirya musu liyafa, suka ci suka sha.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ