Dukan ƙasa za ta zama kibritu da gishiri, ba shuka, ba amfani, ciyawa kuma ba ta tsirowa, kamar yadda Ubangiji ya kabantar da Saduma da Gwamrata, da Adam da Zeboyim, da zafin fushinsa.
Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.
“Na hallakar da waɗansunku Kamar yadda na hallakar da Saduma da Gwamrata. Kamar sanda kuke, wanda aka fizge daga wuta. Duk da haka ba ku komo wurina ba.
Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna Allah na Isra'ila, Na rantse cewa, Mowab za ta zama kamar Saduma, Ammonawa kuma za su zama kamar Gwamrata. Za su zama ƙasar ƙayayuwa Da kwazazzaban gishiri marar amfani har abada. Mutanena waɗanda suka ragu za su washe su, su mallake su.”
“Ƙaƙa zan iya rabuwa da ke, ya Ifraimu? Ƙaƙa zan miƙa ki, ya Isra'ila? Ƙaƙa zan maishe ki kamar Adma? Ƙaƙa zan yi da ke kamar Zeboyim? Zuciyata tana motsawa a cikina, Juyayina ya huru.
Abin da zai faru ga Edom zai zama daidai da abin da ya faru ga Saduma, da Gwamrata, da biranen da suke kusa da su, a lokacin da aka kaɓantar da su. Ba wanda zai zauna cikinta, ba wanda kuma zai yi zaman baƙunci a cikinta, ni Ubangiji na faɗa.
zai ci karo da azabar Allah tsantsa ta tsananin fushinsa, za a kuwa azabta shi da wuta, da duwatsun wuta, a gaban mala'iku tsarkaka, da kuma Ɗan Ragon.
Lutu ya ɗaga idanunsa sama ya dubi kwarin Urdun, ga shi kuwa da dausayi mai kyau ƙwarai, sai ka ce gonar Ubangiji, kamar ƙasar Masar wajen Zowar, tun kafin Allah ya hallaka Saduma da Gwamrata.
“Tsararraki masu zuwa nan gaba, wato 'ya'yan da za su gaje ku, da baƙon da ya zo daga ƙasa mai nisa, za su ga annobar ƙasar, da cuce-cucen da Ubangiji zai ɗora mata.
Amma cikin annabawa na Urushalima, Na ga abin banƙyama. Suna yin zina, suna ƙarya, Suna ƙarfafa hannuwan masu aikata mugunta, Saboda haka ba wanda ya juya ga barin muguntarsa, Dukansu suna kama da Saduma, Mazaunanta kuwa kamar Gwamrata.”