Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Shi wanda ya halicce su, ya ce, “Ba ka da iko ka yi mini tambaya game da 'ya'yana, Ko ka faɗa mini abin da ya kamata in yi!
Sa'ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko'ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”
ga shi, baranka ya sami tagomashi a idonka, ka kuwa nuna mini babban alheri da ka ceci raina, amma ba zan iya in kai tuddan ba, kada hatsarin ya same ni a hanya, in mutu.