Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 19:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Sa'ad da safiya ta gabato, mala'ikun suka hanzarta Lutu, suna cewa, “Tashi, ka ɗauki matarka da 'ya'yanka biyu mata da suke nan, don kada a shafe ku saboda zunubin birnin.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Gari na wayewa, sai mala’ikun nan suka ƙarfafa Lot suna cewa, “Yi sauri! Ka ɗauki matarka da ’ya’yanka biyu mata waɗanda suke a nan, don kada a shafe ku sa’ad da ake hukunta birnin.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 19:15
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai na ji wata murya daga Sama, tana cewa, “Ku fito daga cikinta, ya ku jama'ata, Kada zunubanta su shafe ku, Kada bala'inta ya taɓa ku.


Domin ya ce, “Na saurare ka a lokacin samun karɓuwa, Na kuma taimake ka a ranar ceto.” Ga shi, yanzu ne lokacin samun karɓuwa! Ga shi kuma, yau ce ranar ceto!


Gaggauta, ka gudu zuwa can, ba zan yi kome ba sai ka isa wurin.” Domin haka aka kira sunan garin Zowar.


Sa'ad da suka fitar da shi, suka ce, “Ka gudu domin ranka, kada ka waiwaya baya, ko ka tsaya ko'ina cikin kwari, gudu zuwa tuddai domin kada a hallaka ka.”


Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri 'ya'yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.


Amma da ya yi ta ja musu rai, sai mutanen suka kama hannunsa, da na matarsa, da na 'ya'yansa biyu mata, saboda jinƙan da Ubangiji ya yi masa, suka fitar da shi suka kai shi a bayan birnin.


Shi zai hukunta su saboda muguntarsu, Ya hallaka su saboda zunubansu. Ubangiji Allahnmu zai hallaka su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ