Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 18:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji. Da a ce za a sami ashirin a wurin fa?” Ya amsa ya ce, “Sabili da ashirin ɗin ba zan hallaka shi ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Ibrahim ya ce, “Yanzu fa da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, in ashirin kaɗai aka samu a can fa?” Ya ce, “Saboda ashirin ɗin, ba zan hallaka shi ba.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 18:31
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari.


a koyaushe kuna addu'a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fāsawa. A kan wannan manufa ku tsaya da kaifinku da matuƙar naci, kuna yi wa dukan tsarkaka addu'a.


Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai.


Ina gaya muku, ko da yake ba zai tashi ya ba shi wani abu don yana amininsa ba, amma saboda nacinsa zai tashi ya ba shi ko nawa yake bukata.


To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?


“Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.


Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji, ni da nake ba kome ba ne, amma turɓaya ne da toka.


Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan yi magana. Da a ce za a sami talatin a wurin fa?” Ya amsa, “Ba zan yi ba, in na sami talatin a wurin.”


Sai ya ce, “Kada dai Ubangiji ya husata, zan sāke yin magana, sau ɗayan nan kaɗai. Da a ce za a sami goma a wurin fa?” Ya amsa ya ce, “Sabili da goma ɗin ba zan hallaka shi ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ