Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 18:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji, ni da nake ba kome ba ne, amma turɓaya ne da toka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Sai Ibrahim ya ƙara cewa, “Yanzu da na yi karambani har na yi magana da Ubangiji, ko da yake ni ba kome ba ne illa turɓaya da toka,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 18:27
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai na ce, “Sa zuciyata ya ƙare! Na shiga uku! Kowace maganar da ta fito bakina zunubi ce, ina zaune a tsakanin mutane waɗanda duk maganarsu zunubi ce, ba ta da tsarki. Amma yanzu da idona na ga Sarki, Ubangiji Mai Runduna!”


Da Bitrus ya ga haka, sai ya fāɗi a gaban Yesu ya ce. “Ya Ubangiji, wane ni da za ka tsaya kusa da ni, domin ni mutum ne mai zunubi.”


Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.” (2Tas 3.10; Far 2.7; Zab 90.3; 104.29; M.Had 12.7)


Ya kuma ba su wani misali cewa ya kamata kullum su yi addu'a, kada kuma su karai.


Amma kai ne Ubanmu, ya Ubangiji. Mu kamar yumɓu ne, kai kuwa kamar maginin tukwane. Kai ka halicce mu,


sa'an nan turɓaya ta koma ƙasa kamar a dā, ruhu kuma ya koma wurin Allah wanda ya ba da shi.


Allah ya jefar da ni cikin laka, Na zama kamar ƙura ko toka.


Ta ƙaƙa zai amince da talikinsa wanda aka yi da ƙasa, Abin da yake na ƙura, ana kuwa iya murƙushe shi kamar asu.


Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.


Ya Ubangiji wane ne mutum, har da kake lura da shi? Wane ne ɗan adam kurum, har da kake kulawa da shi?


Wane ne mutum, har da kake tunawa da shi, Mutum kurum, har da kake lura da shi?


Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.


Da a ce za a rasa biyar daga cikin adalai hamsin ɗin, za ka hallaka birnin duka saboda rashin biyar ɗin?” Sai ya ce, “Ba zan hallaka shi ba in na sami arba'in da biyar a wurin.”


Amma Musa ya roƙi Ubangiji Allahnsa, ya ce, “Ya Ubangiji, me ya sa ka husata da mutanenka waɗanda ka fisshe su da ƙarfin ikonka mai girma daga ƙasar Masar?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ