Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 18:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Wannan ya yi nesa da kai, da ka aikata irin haka, wato da za ka aza mai adalci daidai yake da mugu! Wannan ya yi nesa da kai! Mahukuncin dukan duniya ba zai yi adalci ba?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba, ka kashe masu adalci tare da masu mugunta, ka ɗauka masu adalci da masu mugunta daidai? Tabbatacce ba za ka taɓa aikata irin wannan abu ba! Mai hukuncin dukan duniya ba zai aikata gaskiya ba?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 18:25
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Allah bai taɓa yin danniya ba, Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba.


“Amma daɗai Allah ba zai rabu da amintattu ba, Ba kuwa zai taɓa taimakon mugun mutum ba.


Mutane za su ce, “Hakika an sāka wa adalai, Hakika akwai Allah wanda yake shara'anta duniya!”


“Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne, Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne. Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi, Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.


Kai ne mai yi wa dukan mutane shari'a, Ka tashi, ka sāka wa masu girmankai Abin da ya dace da su!


Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.


Sa'an nan za ku ga bambanci tsakanin masu adalci da mugaye, da tsakanin mutumin da yake bauta mini da wanda ba ya bauta mini.”


A gaban Ubangiji, gama ya zo ne ya yi mulki bisa duniya! Zai yi mulki bisa dukan jama'ar duniya da adalci da gaskiya.


Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka. Duk da haka zan bayyana ƙarata a gabanka, Me ya sa mugaye suke arziki cikin harkarsu? Me ya sa dukan maciya amana suke zaman lafiya, Suna kuwa ci gaba?


A kwanakina marasa amfani na ga kowane irin abu. Adali ba safai yakan yi tsawon rai ba, mugu kuwa yakan yi tsawon rai a mugayen ayyukansa.


Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu suke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala.


Da a ce, akwai masu adalci hamsin cikin birnin, za ka hallaka wurin, ba za ka yafe su saboda masu adalcin nan hamsin waɗanda suke cikinsa ba?


“A wannan lokaci kuma na umarci shugabanninku na ce, ‘Ku yi adalci cikin shari'a tsakanin 'yan'uwanku, tsakanin mutum da ɗan'uwansa, ko kuma da baren da yake zaune tare da shi.


Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’


Don haka ni ban yi maka laifi ba, kai ne kake yi mini laifi da kake yaƙi da ni. Ubangiji ne alƙali yau, zai shara'anta tsakanin Isra'ilawa da Ammonawa.”


Yanzu fa ku yi tsoron Ubangiji. Ku lura da abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu bai yarda da rashin yin adalci ba, ko son zuciya, ko karɓar rashawa.”


Ka yi daidai da ka hukunta mu haka! Kai mai aminci ne, mu kuwa mun yi zunubi.


“Saboda haka ku kasa kunne gare ni, ku da kuke haziƙai, Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne, A wurin Mai Iko Dukka ba kuskure,


Sai na ce a zuciyata, “Da adali, da mugu, Allah zai shara'anta su, domin an ƙayyade lokaci na yin kowane abu da na yin kowane aiki.”


Amma ya Ubangiji Mai Runduna, mai shari'ar adalci, Kakan gwada zuciya da tunani, Ka yarda mini in ga sakayyar da za ka yi mini a kansu, Gama a gare ka na danƙa maganata.


“Amma kun ce, ‘Hanyar Ubangiji ba daidai ba ce.’ Ku ji ya ku mutanen Isra'ila, hanyata ba daidai ba ce? Ashe, ba hanyarku ce ba daidai ba?


Sai Musa da Haruna suka fāɗi rubda ciki, suka ce, “Ya Allah, Allahn ruhohin 'yan adam duka, za ka yi fushi da dukan taron jama'a saboda zunubin mutum ɗaya?”


Itatuwa a jeji za su yi sowa domin murna Sa'ad da Ubangiji zai zo ya yi mulki a duniya.


Gaskiya ce, Allah ba zai aikata mugunta ba, Mai Iko Dukka ba zai kauce wa adalci ba.


Idan mutane ba su tuba ba, Allah zai wasa takobinsa,


Sammai suna shelar adalcin Allah, Domin shi yake yin shari'a!


Ko da duniya da dukan waɗanda yake zaune cikinta za su ɓace, Zan ƙarfafa harsashin gininta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ