Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Farawa 18:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Sai kuma Ubangiji ya ce, “Tun da yake kuka a kan Saduma da Gwamrata ya yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni ƙwarai,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kuka a kan Sodom da Gomorra ta yi yawa, zunubinsu kuma ya yi muni sosai,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Farawa 18:20
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

gama muna gab da hallaka wurin nan, domin kukan da ake yi a kan mutanen ya yi yawa a gaban Ubangiji. Ubangiji kuwa ya aiko mu, mu hallaka birnin.”


Ayyukansu na son zuciya za su zama shaida gāba da su. Suna ta aikata zunubi a fili, kamar yadda mutanen Saduma suka yi. Sun shiga uku, su ne kuwa suka jawo wa kansu.


Mutanen Saduma kuwa mugaye ne masu aikata zunubi ƙwarai gāba da Ubangiji.


Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa.


Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.


Irmiya ya ce, “Ko da yake zunubanmu su ne shaidunmu, Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda sunanka! Gama kāsawarmu ta yi yawa, Domin mun yi maka zunubi.


Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da yake daidai, Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!


Amma kafin su shiga barci, mutanen birnin Saduma, samari da tsofaffi, dukan mutane gaba ɗaya suka kewaye gidan.


Amma cikin annabawa na Urushalima, Na ga abin banƙyama. Suna yin zina, suna ƙarya, Suna ƙarfafa hannuwan masu aikata mugunta, Saboda haka ba wanda ya juya ga barin muguntarsa, Dukansu suna kama da Saduma, Mazaunanta kuwa kamar Gwamrata.”


“'Yarki ita ce Samariya wadda take zaune da 'ya'yanta mata wajen arewa da yake. Ƙanwarki ita ce Saduma wadda take zaune kudu da ke tare da 'ya'yanta mata.


Su sa lauje gama hatsin ya isa girbi. Su shiga su tattaka, Gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika. Manyan randuna sun cika suna tumbatsa, Gama muguntarsu da yawa take.”


“Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka faɗakar da su, gama na ga irin muguntarsu.”


Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ