Nan gaba ba sauran in ce da ku bayi, don bawa bai san abin da ubangijinsa yake yi ba. Sai dai in ce da ku aminai, domin na sanar da ku duk abin da na jiyo wurin Ubana.
Aka kuma cika Nassin nan da ya ce, “Ibrahim ya gaskata Allah, bangaskiyar nan tasa kuma aka lasafta ta adalci ce a gare shi,” aka kuma kira shi aminin Allah.
Sa'ad da ta isa wurin annabi Elisha a kan dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo zai ture ta. Amma mutumin Allah ya ce masa, “Ƙyale ta kurum, gama tana da baƙin ciki ƙwarai, Ubangiji kuwa ya ɓoye mini abin.”