Farawa 18:14 - Littafi Mai Tsarki14 Akwai abin da zai fi ƙarfin Ubangiji? A ajiyayyen lokaci zan komo wurinka, cikin wata tara, Saratu kuwa za ta haifi ɗa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Akwai abin zai gagari Ubangiji? Zan komo wurinka a ƙayyadadden lokacin nan shekara mai zuwa kuma Saratu za tă haifi ɗa.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
“Don me mutanena ba su amsa ba Sa'ad da na je wurinsu domin in cece su? Don me ba su amsa ba sa'ad da na yi kiransu? Ba ni da isasshen ƙarfin da zan fanshe su ne? Ina da iko in sa teku ya ƙafe ta wurin umarnina, Ina kuma da iko in sa rafuffukan ruwa su zama hamada, Kifayen da suke ciki su mutu saboda rashin ruwa.