Sa'ad da harshen wutar ya hau zuwa samaniya daga bagaden, sai mala'ikan Ubangiji ya hau zuwa sama ta cikin harshen wutar bagaden. Manowa da matarsa sun gani, suka fāɗi a fuskokinsu a ƙasa.
Mala'ikan Ubangiji kuwa ya miƙa kan sandan da yake hannunsa, ya taɓa naman da wainar, sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da wainar. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ɓace masa.